Lakurawa Sun Kutsa Cikin Wasu Masallatai A Jihar Neja, Ana Zargin Sun Fara Yaɗa Akidar Tsattsauran Ra’ayi

0 171

Ana zargin ƙungiyar Lakurawa da kutsa cikin wasu masallatai a jihar Neja, inda rahotanni ke cewa sun fara gabatar da wa’azi masu ɗauke da akidar tsattsauran ra’ayi.

Majiyoyi sun bayyana cewa lamarin ya jefa al’umma cikin fargaba, yayin da mazauna yankunan da abin ya shafa ke nuna damuwa kan yiwuwar faɗaɗar ayyukan ƙungiyar zuwa wasu ƙananan hukumomi na jihar.

Rahotanni sun ce ana zargin wasu mambobin ƙungiyar da yin amfani da wa’azi da karatuttukan addini wajen yaɗa manufofinsu, lamarin da ya ƙara tayar da hankalin jama’a.

Ya zuwa yanzu, hukumomin tsaro ba su fitar da cikakken bayani kan lamarin ba, sai dai ana sa ran za su ƙara tsaurara matakan tsaro da sa ido a yankunan da abin ya shafa domin dakile duk wata barazana ga zaman lafiya da tsaron al’umma.

Leave a Reply