Lauya Ya Ce Wanda Ya Rasa Tikiti Ba Zai Iya Komawa Wata Jam’iyya Ya Yi Takara Ba

0 165

Wani lauya mai suna Abdul-Hadee Isah Ibraheem ya bayyana cewa a cewarsa, duk wanda bai samu tikiti a jam’iyyarsa ba ba zai iya komawa wata jam’iyya domin yin takara ba, duba da tanadin dokar zaɓe da kuma jadawalin INEC na zaɓen fidda gwani.

Lauyan ya ce Section 77 na Dokar Zabe (Electoral Act) ya tanadi cewa kowace jam’iyya dole ta miƙa wa INEC sunayen mambobinta akalla kwanaki 21 kafin gudanar da zaɓen fidda gwani. A cewarsa, ranar 10 ga Mayu 2026 ita ce ranar ƙarshe da INEC ta ware domin yin rijista ko sauya sheka daga wata jam’iyya zuwa wata.

Ya ƙara da cewa:

“Daga ranar 10 May 2026 babu wanda zai iya komawa cikin wata jam’iyya, dan haka duk wanda sunan sa baya cikin jam’iyya kafin ranar 10 May 2026 ba zai iya shiga cikin jam’iyyar yayi takara daga baya ba, ba zai iya zaba ba kuma ba za’a iya zaban sa ba”.

Abdul-Hadee Isah Ibraheem ya kuma bayyana cewa INEC ta ware lokacin gudanar da zaɓen fidda gwani daga 23 ga Afrilu 2026 zuwa 30 ga Mayu 2026.

Kalaman lauyan na zuwa ne yayin da ake ta hasashen yiwuwar wasu ’yan siyasa da magoya bayansu sauya sheka zuwa wasu jam’iyyu bayan rikice-rikicen cikin gida da suka biyo bayan zaɓen fidda gwani.

Leave a Reply