Ma’aikatar harkokin Kasashen waje ta ce gobe take sa ran za ta karbi kashin farko na ‘yan Najeriya da aka kwaso daga kasar Ukraine

0 83

Ma’aikatar harkokin Kasashen waje ta sanar da cewa, a gobe ne ake sa ran za ta karbi kashin farko na ‘yan Najeriya da aka kwaso daga kasar Ukraine.

Babban sakataren ma’aikatar, Gabriel Aduda ne ya sanar da hakan.

A cewar Gabriel Aduda, jiragen da aka yi hayar su, Air Peace da Max Air, za su tashi a yau domin dauko ‘yan Najeriya da za kwaso zuwa gida.

Ya kara da cewa, ofisoshin jakadancin Najeriya a kasashen Hungary, Poland, Romania da Slovakia sun karbi ‘yan Najeriya daga kasar Ukraine.

Gabriel Aduda ya sanar da cewa Max Air zai kwaso Dalibai 560 daga Romania yayin da Air Peace zai kwaso mutane 364 daga Poland da 360 daga Hungary.

A ranar Litinin ne gwamnatin tarayya ta bayyana cewa daga yau za ta fara kwaso ‘yan Najeriya daga kasar Ukraine.

Leave a Reply

%d bloggers like this: