‘Nan ba da dadewa ba za a janye yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i ta ASUU ke yi’ – Ministan kwadago

0 109

Ministan kwadago da ayyukan yi Dr. Chris Ngige ya sake bayyana fatan ganin nan ba da dadewa ba za a janye yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i ta ASUU ke yi.

Ministan wanda ya yi magana a wajen zaman ganawar sulhu da aka koma tsakanin gwamnati da wakilan kungiyar malaman a jiya da yamma, ya ce taron zai kare ne da daukar mataki kamar yadda kungiyar ta bukata.

Kungiyar ta kuma kara Jaddada matsayar ta, gabanin taron, inda ta ce ba ta da sha’awar sanya hannu kan duk wata yarjejeniya, amma ya kamata gwamnati ta tabbatar da gaskiyar ta kan yarjejeniyoyin da aka kulla a baya ta hanyar aiwatar da su cikin gaggawa.

Shugaban ASUU na kasa, Emmanuel Osodeke, ya ce kungiyar ta dade tana hada hannu da gwamnati kuma ta kulla yarjejeniyoyin da suka kulla cikin shekaru biyar da suka gabata amma ba a aiwatar da mafi yawan yarjejeniyoyi ba.

Osodeke ya dage cewa za a iya biyan dukkan bukatun kungiyar cikin kankanin lokaci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: