Ma’aikatar kasa da safiyo ta jihar Jigawa ta bayar da wa’adin watanni uku ga masu filotai da basu gina ba

0 65

Ma’aikatar kasa da safiyo ta jihar Jigawa ta bayar da wa’adin watanni uku ga masu filotai da basu gina ba a wasu wurare a birnin Dutse dasu hanzarta ginawa ko kuma hukumar ta kwace su.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Zartarwa na Hukumar Raya Birane ta jiha Adamu Sale Muhammad ya fitar a madadin kwamishinan ma’aikatar.

Yace wadanda umarnin ya shafa sun hadar da masu filotai daga bangaren hagun da dama daga shataletalen mai kwarya zuwa shataletalen gidan gwamnati da masu fulotai daga hagu da dama daga shataletalen gidan gwamnati na pentagon zuwa mahadar unguwar Gadadin wanda ya kunshi fulotan rukunin unguwannin Hybro da na bayan gidajen kwamishinoni.

Adamu Sale ya kara da cewar an baiwa wadanda suka mallakin filotan watanni uku dasu gina su ko kuma a soke rijistar mallakar fulotan da aka basu kamar yadda yake kunshe a takardar mallakar fili.

Leave a Reply

%d bloggers like this: