Ma’aikatar Raya Kiwo ta bayyana kudirinta na inganta kayan aiki a Cibiyar Binciken Dabbobi ta Kasa – VOM

0 160

Ma’aikatar Raya Kiwo ta Tarayya ta bayyana kudirinta na sabunta da kuma inganta kayan aiki a Cibiyar Binciken Dabbobi ta Kasa da ke Vom, kusa da Jos.

Ministan Raya Kiwo, Malam Idi Maiha, ne ya bayyana hakan yayin wata ziyarar aiki da ya kai cibiyar a ranar Juma’a, inda ya ce wannan yunkuri na cikin ajandar “Sabun ta Fata” na Gwamnatin Tarayya don inganta ayyuka.

Ya ce wasu daga cikin kayan aikin cibiyar sun yi tsofan gaske har wasu ma sun fi shi shekaru, sai dai kokarin ma’aikatan ne ke sanya aikin ci gaba.

Ministan ya ce tare da fara aiwatar da shirin sauya fasalin kiwo a filin kiwo na Wase a Jihar Filato, ya zama wajibi a sabunta wannan cibiya domin tana taka muhimmiyar rawa wajen sarrafa rigakafin cututtuka, bincike, da dakile yaduwar cututtuka tsakanin dabbobi.

Leave a Reply