Mabiyan Sheikh Abduljabbar Sun Nemi A Bar Kotu Tayi Aikin Ta Ba Tare Da Tsangwama Ba

0 105

Mabiyan Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara sun yi tir da wani yunkuri da suke zargin ana yi na kawo cikas ga karan  da ya daukaka kan hukuncin kisa da kotu ta yanke masa.

Ibrahim Abdullahi Warure, wanda ya yi magana a madadin mabiyan a wani taron manema labarai  jiya Lahadi a Kano, ya zargi wasu malamai da yin munafurci domin yin watsi da karar.

A cewar Warure, Malaman suna kara matsa lamba ga gwamnati mai jiran gado da kuma kotu da su goyi bayan hukuncin kisan da aka yanke masa.

Ya ce mabiyan za su ci gaba da daukaka karar a gaban babbar kotun Jihar Kano har sai an yi wa malamin nasu adalci.

A cewarsa, wannan hakki ne da ba za a tauye wa malamin ba kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada.

Ya shawarci malaman da yake zargi da su bar kotu ta yi aikinta ba tare da tsangwama ba.

An daure malamin ne a ranar 17 ga watan Yuli, 2021 a gidan yari bisa samun sa da laifin yin kalaman batanci ga Manzon Allah (SAW). Daga bisani kuma wata kotun shari’ar Musulunci da ke Kano ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya a ranar 15 ga watan Disamba, 2022.

Leave a Reply

%d bloggers like this: