Mahaifin Gwamnan Adamawa Ya Rasu

0 166

Alhaji Umaru Badami, mahaifin Gwamna Ahmadu Fintiri na Adamawa ya rasu. Mista Badami, ɗan shekara 82, ya rasu ne ranar Lahadi bayan wata gajeruwar rashin lafiya.

Solomon Kumangar, Darakta Janar na Huɗɗa da Kafafen Watsa Labarai da Sadarwa na Gwamnan ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN rasuwar a Yola.

Ya ce da misalin ƙarfe 2:30 ne Mista Badami ya rasu. “An kwantar da shi a Cibiyar Kula da Lafiya ta Gwamnatin Tarayya dake Yola, jiya aka sallame shi, bayan an sallame shi ne sai ya faɗi”, in ji Mista Badami.

Mamacin, wanda tsohon soja ne mai ritaya, ya bar mata ɗaya da ‘ya’ya shida, da suka haɗa da Gwamna Fintiri.NAN ya ruwaito cewa tuni aka binne Mista Badami kamar yadda Musulunci ya tanada, bayan an yi sallar Jana’iza a Babban Masallacin Yola.

Leave a Reply

%d bloggers like this: