Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yace mahara wadanda suke kashewa da sace yan Najeriyan da basu ji ba, basu gani ba, ‘yan ta’adda ne da ya kamata a hukunta su akan haka.

Buhari wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikatansa, Farfesa Ibrahim Gambari, ya sanar da haka a jiya a wajen wani zaman ganawa kan tsaro a Kaduna, wanda ya samu halartar gwamnonin Arewa 19 da Sufeto Janar na Yansandan Kasa, Mohammed Adamu, da darakta janar na hukumar tsaro ta DSS, Yusuf Bichi, da ministan labarai da al’adu, Lai Mohammed.

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar na 3, shine ya jagoranci sarakuna daga dukkan sassan Arewa, zuwa wajen zaman ganawar.

Shugaban kasar, ta bakin shugaban ma’aikatansa, yace gwamnatinsa zata cigaba da fatattakar yan ta’addan, da mahara da masu garkuwa da mutane. A nasa bangaren, Sarkin Musulmi, ya bukaci yan Arewa da su zama masu hakuri da gwamnoninsu.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: