Majalisar ƙasa ta ce zata cigaba da tallafawa shugaba Buhari domin ciyar da Najeriya gaba

0 234

Majalisar Kasa ta ce zata cigaba da tallafawa shugaban Kasa Muhammadu Buhari, domin ciyar da kasar nan gaba tare da cika Alkawarirrikan da ya daukawa yan Najeriya.

Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmed Lawan, ya bayyana hakan ne a jiya Lahadi a garin Gombe, lokacin da yake kaddamar rabon kayayyakin dogaro da kai wanda Sanata Sa’idu Ahmed Alkali, Sanatan Gombe ta Arewa ya raba.

Sanata Ahmed Lawan, ya ce Gwamnatin Jam’iyar APC karkashin Jagorancin Shugaba Buhari ta samarda shugabanci na gari ga kasar nan, tare da kawo cigaba a Najeriya.

Dr Ahmed Lawan, ya ce shugaba Buhari ya na da kudurin ciyar da kasar nan gaba, kuma ya cigaba da jajircewa akan hakan, inda ya kara da cewa Shugaba Buhari ya cancanci yabawa, bisa yadda yake duk mai yuwuwa domin bunkasa kasa.

Kazalika, ya bukaci yan Najeriya da kada su yarda a yaudare su a lokacin yakin neman zabe, inda ya nanata cewa Gwamnatin APC tana cigaba da samarda roman demokradiya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: