Cibiyar NCDC ta ce sabbin mutane 404 ne suka sake harbuwa da cutar Corona a Najeriya

0 121

Cibiyar Dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC ta ce sabbin mutane 404 ne suka harbu da cutar Corona a kasar nan a jiya.

Hukumar ta NCDC ta ce an samun bullar cutar ne a jikkunan mutanan da suka fito daga Jihohi 11 na kasar nan ciki harda birnin tarayya Abuja.

NCDC ta ce an salami mutane 15 wanda suka warke daga cutar a cibiyoyin da ake kula dasu.

Haka kuma an samu mutum 1 da cutar ta hallaka a jiya wanda hakan ya kawo adadin mutanen da cutar ta hallaka zuwa dubu 2,985.

Kawo yanzu adadin mutanen da suka harbu da cutar Corona tun bayan bayyanarta a kasar nan sun kai dubu 223,887.

Leave a Reply

%d bloggers like this: