Gwamna Ganduje yace rikicin dake addabar jam’iyyar APC a Kano bazai hana gwamnatinsa gudanar da ayyukan cigaban jihar ba

0 122

Gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje yace rikicin dake addabar jam’iyyar APC a jihar bazai kawar da hankalin gwamnatinsa ba daga gudanar da ayyukan cigaban jihar.

Gwamna Ganduje, kamar yadda yazo a sanarwar da babban sakataren yada labaransa, Abba Anwar, ya fitar, ya fadi haka jiya a Gidan Gwamnatin Kano yayin wani taron masu ruwa da tsaki.

Yace an gudanar da taron ne domin jaddada bukatar zaman lafiya a jam’iyyar. Taron ya samu halartar Sanata Kabiru Gaya, da ‘yan majalisar wakilai, da kakakin ‘yan majalisar dokokin jihar Kano, da sauransu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: