Bankin AfDB zai rantawa Najeriya da Dala miliyan 210 domin bunƙasa harkar noma

0 149

Bankin Raya Kasashen Afirka na AfDB ya amince da shirin baiwa Najeriya rancen Dala miliyan 210 domin inganta ayyukan noman zamani a cikin wasu jihohin kasar wanda ake saran miliyoyin jama’a zasu amfana da shi.

Sanarwar da Bankin mai Cibiya a Abidjan ya gabatar tace rance shine kashi na farko a shirin da zasu hada kai da gwamnatin Najeriya wajen ganin an bunkasa ayyukan noma da samar da abinci.

Bankin ya bayyana shirin a matsayin wanda zai bude kofar arzikin noman da Najeriya ke da shi da kuma bunkasa masana’antu wajen samar da amfanin gonar da kuma kiwo.

Wani manomi na aikin a gonar sa a Najeriya
Wani manomi na aikin a gonar sa a Najeriya Fati Abubakar/RFI

Sanarwar Bankin yace a karkashin shirin na farko Jihohin Imo da Cross River da Abuja zasu amfana da tallafin kiwon dabbobi domin samar da nama da kuma madara, sai kuma Jihar Kadauna wadda zata amfana da shirin samar da tumatir da masara da kuma citta.

Jihar Kano zata amfana da tallafin noman shinkafa da tumatir da gyada da kuma ridi, sai Kwara wadda zata amfana da shirin kiwo.

Wasu Shanu mallakin Fulani makiyaya yayin kiwo a wani yanki dake wajen jihar Kaduna.
Wasu Shanu mallakin Fulani makiyaya yayin kiwo a wani yanki dake wajen jihar Kaduna. AFP/Getty Images – Stefan Heunis

Sauran sun hada da Jihar Ogun wadda zata amfana da tallafin noman rogo da shinkafa da kuma kiwon kaji da kifi, sai Jihar Oyo wadda zata samu tallafin noman rogo da waken soya da kuma shinkafa.

Bankin yace wannan tallafin na daga cikin manyan shirye shiryen sa na taimakawa jama’a wajen dogaro da kan su.

Tashe tashen hankula sun yi matukar illa ga shirin noma da kiwo a Najeriya musamman rikicin manoma da makiyaya da kuma Yan bindiga barayin shanu wadanda ke sace dabbobin jama’a da kuma hana manoma zuwa gonakin su.

Source: RFI Hausa

Leave a Reply

%d bloggers like this: