Majalisar Dattawa ta bukaci Shugaba Buhari ya ayyana ‘yan fashin daji a matsayin ‘yan ta’adda

0 77

Majalisar Dattawa ta bukaci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya ayyana ‘yan fashin dajin da suka addabi yankin arewacin kasarnan a matsayin ‘yan ta’adda, tare da ayyana yaki a kansu.

Majalisar ta kuma bukaci a shafe su daga doron duniya, ta hanyar fara tarwatsa wuraren fakewarsu da jefa musu bama-bamai.

‘Yan Majalisar Dattawan na kuma son shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya bayyana shugabannin ‘yan fashin dajin a matsayin wadanda ake nema ruwa a jallo, domin kamo su a hukunta su.

An amince da wannan matsaya ne, bayan wani kuduri da daya daga cikin ‘yan majalisar Sanata Ibrahim Abdullahi Gobir ya gabatar, da hadin guiwar wasu takwarorinsa takwas.

Abdullahi Gobir yayi nuni da cewa, majalisar dan majalisar dattawa ta Sokoto ta zama mafakar ‘yan fashin daji, saboda fatattakarsu da ake yi a jihar Zamfara.

Leave a Reply

%d bloggers like this: