Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Juma’a a matsayin ranar hutu domin tunawa da ranar da Najeriya ta samu yancin kanta

0 82

Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Juma’a 1 ga watan Octoba a matsayin ranar hutu domin tunawa da ranar da Najeriya ta samu yancin kanta shekaru 61 da suka gabata.

Ministan Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida, Mista Rauf Aregbesola, shine ya bayyana hakan a madadin gwamnatin tarayya, kamar yadda hakan yake cikin wata sanarwa da Babban Sakatare a ma’aikatar Dr Shuaibu Belgore ya fitar.

Sanarwar ta ce Ministan ya taya yan Najeriya murna kan cikar kasar nan shekaru 61 da samun yan cin kai, inda ya kara bawa yan Najeriya tabbacin cewa gwamnatin tarayya zata yi duk mai yuwuwa domin ganin ta magance matsalolin da suke addabar kasar nan.

Ministan ya ce, gudanar da bukukuwan cikar Najeriya shekaru 61 da samun yan cin kai ya zama dole, sai dai kuma hakan bazai yiwuwa, biyo bayan bullar Nau’in cutar Corona ta Delt Variance.

Kazalika, ya bukaci yan Najeriya na ciki da wajen kasar nan su hada hannu wuri guda tare da gwamnatin shugaban Kasa Muhammadu Buhari, domin tabbatar da cewa sun ciyar da kasar nan gaba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: