Gwamna Nasir El-Rufai yace bai yarda da tsarin karba-karba a shugabancin Najeriya

0 83

Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya yi karin haske kan matsayar Kungiyar Gwamnonin Arewa game da tsarin karba-karba.

A wani taro da suka yi a Kaduna ranar Litinin, gwamnonin sun ce tsarin karba-karba ya sabawa kundin tsarin mulkin Najeriya.

Sun fadi hakan ne a matsayin martani ga bukatar takwarorinsu na Kudancin da suka bukaci yankinsu ya samar da shugaban Kasa na gaba.

A tattaunawarsa da wasu zababbun ‘yan jarida, El-Rufai ya ce babu wanda ya isa ya dauka cewa zai iya zama a Legas ko Fatakwal ya yanke shawarar abin da Arewa za ta yi ko kuma wanda Arewa za ta zaba.

Ya ce idan kudu na son mulki, ya kamata ta shirya zama da Arewa a tattauna sannan a amince kan wanda ya kamata a zaba amma ba amfani da tilas ba don neman komawar mulki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: