Majalisar dattawa ta yi shiru na minti daya domin tunawa da tsohon hadimin shugaban kasa, Ahmed Gulak

0 117

A wani labarin mai alaka da wannan, majalisar dattawa ta yi shiru na minti daya domin tunawa da tsohon hadimin shugaban kasa, Ahmed Gulak, wanda aka yiwa kisan wulakanci a ranar Lahadi a Owerri, babban birnin jihar Imo.

Hakan ya biyo bayan kudirin da mataimakin shugaban majalisar dattawa kuma shugaban kwamitin gyaran kudin tsarin mulki, Ovie Omo-Agege, a zauren majalisar ta dattawa.

A wani labarin kuma, kungiyar gwamnonin kudu maso gabas ta bukaci hukumomin tsaro da su gaggauta kamo wadanda ke da hannu a kisan Ahmed Gulak.

Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da aka fitar a yau ta hannun shugaban kungiyar kuma Gwamnan jihar Ebonyi,David Umahi, bayan wani zaman ganawa ta internet da aka gudanar dangane da halin tsaro a yankin.

Kungiyar ta bayyana kisan da aka yiwa Ahmed Gulak da cewa babban kalubalene ga kasa.

Gwamnonin sun yi ta’aziyya ga iyalan Ahmed Gulak, da gwamnatin jihar Adamawa da kuma ‘yan Najeriya baki daya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: