Wasu ‘yan bindiga sun kashe mutane 12 a kauyuka daban-daban na karamar hukumar Ado ta jihar Benue.

Shaidun  gani da ido sun ce an kaddamar da harin akan kauyukan lokaci guda a tsakanin Asabar da dare da sanyin safiyar Lahadi a kauyen Tologa da Ndi-Obasi da Odoken dukkansu a mazabar Ekile dake gundunar Ijigban a karamar hukumar Ado.

Shugaban karamar hukumar, James Oche, ya gayawa yan jarida a Makurdi ta wayar tarho cewa an kashe mutane 12 a harin da aka kitsa a kan kauyuka 5 a karamar hukumarsa.

Oche yayi zargin cewa harin na ramuwar gayya daga wadanda ake zargin makiyaya ne, bayan wasu mutane da ake zargin ‘yan kungiyar IPOB ne sun tsallako daga jihar Ebonyi zuwa karamar hukumarsa ta Ado a jihar Benue suka kashe wani dattijo dan Fulani mai suna Muhammad Isa.

Da aka tuntube shi, mai magana da yawun rundunar yansandan jihar Benue, DSP Catherine Anene, bata amsa kiran wayarta ba har ya zuwa lokacin da aka hada wannan rahoton.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: