Majalisar Jigawa ta dakatar da shugaban ƙaramar hukumar Buji
Majalisar Dokokin Jihar Jigawa ta dakatar da Shugaban Ƙaramar Hukumar Buji, Hon. Najibullahi Falalu Tukur, bisa zargin rashin ɗa’a da kuma almundahanar kuɗaɗen gwamnati.
Majalisar ta ɗauki matakin ne bayan ta amince da rahoton Kwamitinta kan Ƙananan Hukumomi a zaman da ta gudanar ranar Talata, 1 ga Satumba, 2026.
Mataimakin Shugaban kwamitin, Hon. Sani Sale Zaburan, ne ya gabatar da rahoton gaban majalisar, inda kwamitin ya ba da shawarar dakatar da shugaban ƙaramar hukumar bisa tanadin Sashe na 36, ƙananan sashe na (2) da (3) na Dokar Kafa Ƙananan Hukumomin Jihar Jigawa ta 2024.
Bayan sanar da dakatarwar, Kakakin Majalisar, Hon. Haruna Aliyu Dangyatin, ya umarci shugaban ƙaramar hukumar da aka dakatar da ya miƙa dukkan kadarorin gwamnati da ke hannunsa ga mataimakinsa.
Kakakin ya kuma sanar da kafa wani Kwamitin Musamman domin gudanar da bincike kan zarge-zargen rashin ɗa’a da kuma almundahanar kuɗaɗen gwamnati da ake yi wa shugaban ƙaramar hukumar.
Aminiya ta ruwaito cewa Hon. Usman Abdullahi Tura Musari, mai wakiltar mazaɓar Guri, shi aka naɗa a matsayin shugaban kwamitin.
Sauran mambobin kwamitin su ne ’yan majalisar da ke wakiltar mazaɓun Maigatari, Malam Madori, Birnin Kudu, Yankwashi, Kafin Hausa da Sule Tankarkar.
Majalisar ta ɗora wa kwamitin alhakin gudanar da cikakken bincike kan zarge-zargen da ake yi wa shugaban ƙaramar hukumar, tare da gabatar da rahoton binciken ga majalisar domin ɗaukar matakin da ya dace.
Bayanai sun ce majalisar ba ta ƙayyade wa’adin dakatarwar ba a yayin da ake jiran kammala binciken kwamitin da kuma matakin da majalisar za ta ɗauka kan sakamakon binciken.