Majalisar Tsaro Ta Jihar Kano Ta Ayyana Kwacen Waya A Matsayin Fashi Da Makami

0 96

Majalisar tsaro ta jihar Kano ta ayyana kwacen waya a matsayin fashi da makami, kuma duk wani mutum ko kungiyar da aka kama da aikata laifin za’a yanke masa hukunci ne a matsayin ‘dan fashi da makami.

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida mai barin gado Muhammad Garba ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai jiya a Kano.

Ya ce majalisar wadda gwamna mai barin gado, Abdullahi Ganduje ya jagoranta, a yayin zamanta na tantancewa, ta lura da laifin da ake aikatawa a ‘yan kwanakin nan ya kai wani matsayi mai cike da damuwa, don haka ya yi kira da a dauki tsattsauran matakai don magance shi.

Muhammad Garba ya kuma bayyana cewa majalisar ta amince da samar da wata runduna ta musamman domin tunkarar matsalolin da ke faruwa a jihar.

Kwamishinan ya kara da cewa majalisar a yayin da take tattaunawa kan rantsar da sabon gwamnan ta ce an dauki dukkan matakan da suka dace don ganin an gudanar da bukukuwan cikin kwanciyar hankali.

Ya kuma gargadi batagarin da ka iya yin amfani da wannan dama wajen haddasa tashin hankali a bukukuwan da su guji aikata irin wannan abu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: