Akalla Shugabannin Kasashe 20 Na Duniya Ciki Har Da Afirka Ne Suka Halarci Bikin Rantsar Da Shugaba Bola Tinubu

0 27

Akalla shugabannin kasashe 20 na duniya ciki har da Afirka ne ke Abuja yanzu haka, domin halartar bikin rantsar da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a matsayin shugaban kasa na 16 a tarihin kasar nan.

Bikin rantsar da Tinubu shi ne karo na 7 a jere na mika mulki a dimokuradiyya a cikin shekaru 24 na dimokuradiyyar Najeriya, bayan komawar mulkin farar hula a 1999.

Sakataren gwamnatin tarayya kuma shugaban kwamitin rikon kwarya na shugaban kasa Boss Mustapha wanda tun da farko ya bayyana shirin kaddamarwar a wani taron manema labarai na duniya a Abuja, ya ce an kammala dukkan shirye-shiryen mika mulki ba tare da wata matsala ba. .

Ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya ta mika goron gayyata ga wasu shugabanni da shugabannin gwamnatoci da kuma shugabannin kungiyoyin kasa da kasa, inda ya ce ya yi farin cikin bayar da rahoton cewa da yawa daga cikin wadanda aka gayyata sun tabbatar da halartar taron da kan su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: