Buhari Ya Sanya Hannu Kan Kudurin Dokar Kafa Hukumar Kula Da Almajirai

0 60

Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya hannu kan kudirin dokar neman a kafa hukumar kula da Almajirai da yaran da ba sa zuwa makaranta domin hana fatara da cin zarafi.

Kudirin da Balarabe Shehu Kakale da wasu mutane 18 suka dauki nauyi mai suna: Kudirin dokar kafa hukumar kula da ilimin almajirai ta kasa da kuma ‘ya’yan da ba su zuwa makaranta domin samar da tsarin ilimi na zamani don magance matsalar jahilci, samar da dabarun koyon sana’o’i da kasuwanci.

Da yake zantawa da manema labarai, dan majalissar da ya gabatar da kudirin kafa hukumar Kakale, Sokoto, ya ce shugaban kasar ya sanya hannu kan kudirin ne a ranar Asabar din da ta gabata a lokacin da ake gudanar da bikin ranar yara ta duniya.

Ya bayyana kudurin dokar a matsayin kyauta ga yan Najeriya.

Kudurin dai ya fuskanci adawa mai tsanani daga bangarori da kungiyoyi daban-daban na kasar tun bayan kaddamar da shi. Duk da haka, an amice da shi bayan karatu na biyu da na uku a majalissar kasar nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: