An Fara Samun Dogayen Layukan Shan Mai A Gidajen Man Kasar Nan

0 70

An fara samun dogayen layukan mai a gidajen mai dake birnin Legas, jim kadan biyo bayan jawabin sabon shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

Kamfanin Dillancin Labarai na kasa NAN ya lura cewa tashoshin NNPC da ke Ikeja, Alausa sun cika da cunkoson ababen hawa inda ake rige-rigen siyen man

Yawancin tashoshi masu zaman kansu ba sa sayarwa har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto.

A jawabinsa na kaddamarwa, Tinubu ya ce tallafin yana amfanar masu hannu da shuni ta hanyar kashe talakawa ne kawai. Ya ce zai kuma sake duba korafe-korafen da ake yi kan yawan harajin da za a samu ta yadda za a bunkasa tattalin arziki da jawo masu zuba jari.

Leave a Reply

%d bloggers like this: