Shugaban Kasa Bola Tinubu Ya Bayyana Bakin Cikinsa Kan Rasuwar Raymond Dokpesi

0 58

Shugaban Kasa Bola Tinubu ya bayyana bakin cikinsa kan rasuwar wanda ya kafa kamfanin sadarwa na Daar Communications, masu gidajen Talabijin na AIT da gidan rediyon Raypower, Raymond Dokpesi.

A wata sanarwa da ta fito daga ofishinsa da yammacin jiya, shugaban kasar ya bayyana mutuwar dan jaridan a matsayin babban rashi ga masana’antar yada labaran Najeriya da ma kasa baki daya.

A wani batun kuma, tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP a zaben shekarar 2023, Atiku Abubakar, shi ma yayi jimamin rasuwar Raymond Dokpesi.

Atiku Abubakar, a cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Paul Ibe, ya fitar, ya bayyana cewa Raymond Dokpesi ya kasance gwani yadda ya sake fasalin harkokin kasuwancin Najeriya a kowane fanni na harkokinsa, inda ya ce ya yi rashin abokin kuma dan uwa. Raymond Dokpesi ya rasu jiya a wani asibitin Abuja. Kuma a jiya ne aka sanar da rasuwarsa a wata sanarwa mai dauke da sa hannun dansa, Raymond Dokpesi Junior.

Leave a Reply

%d bloggers like this: