kasashen Duniya Da Dama Sun Aike Wa Da Shugaba Bola Tinubu Sakon Fatan Alheri

0 71

Kasashen duniya da dama a jiya sun gabatar da sakon fatan alheri da kuma wasikun goyon baya da neman hadin gwiwa ga shugaban kasa Bola Tinubu a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Wata sanarwa da Tunde Rahman daga ofishin shugaban kasar ya fitar jiya ta ce wakilai na musamman da shuwagabannin kasashen duniya ne suka mika wa shugaban kasar wasikun sakonnin bayan rantsar da shi a matsayin shugaban kasar Najeriya na 16.

Daga cikin kasashen akwai Birtaniya, Amurka, Saudi Arabia, Japan, Brazil, Koriya ta Kudu, Isra’ila, Cape Verde, Somalia da kuma Nicaragua.

Yayin da yake taya Bola Tinubu murna, sabon jakadan Burtaniya a Najeriya, Richard Montgomery, ya gabatar da wasiku daga Fira Ministan Burtaniya, Rishi Sunak, da Sarki Charles da Archbishop na Canterbury, Justin Welby. Tawagar Amurka karkashin jagorancin sakatariyar gidaje da raya birane, Marcia L. Fudge, ta kai wa shugaban kasa Bola Tinubu ziyarar ban girma inda suka yi wata gajeruwar tattaunawa da shi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: