Zamu Sake Bibiyar Tuhumar Kisan Da Ake Yiwa Alhassan Ado Doguwa Abba Gida-Gida

0 84

Gwamnan na jihar Kano ya yi alkawarin sake bude tuhumar kisan da ake yi wa dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Tudunwada/Doguwa, Alhassan Ado Doguwa.

A ranar 1 ga watan Maris ne aka fara gurfanar da dan majalisar wakilan a gaban wani babban alkalin kotun majistire bisa zargin kisan kai inda kuma wata babbar kotun tarayya da ke Kano ta ba da belinsa akan kudi naira miliyan 500 a ranar 6 ga watan Maris.

A wani abin mamaki na ba zata, gwamnatin Abdullahi Ganduje a ranar 25 ga watan Mayu, ta wanke dan majalisar daga zargin kisan, inda ta ce ba shi da wata tuhuma da zai amsa.

Sai dai sabon gwamnan jihar da aka rantsar a jawabinsa na farko a jiya ya ce zai ci gaba da shari’ar har zuwa karshenta.

Dangane da annobar kwacen waya, sabon gwamnan ya sanar da kafa wata rundunar hadin gwiwa ta musamman domin hana satar waya da sauran laifukan da ake aikatawa akan tituna.

Leave a Reply

%d bloggers like this: