Gwamnan Jihar Zamfara Yace Zai Hada Kai Da Gwamnatin Tarayya Domin Sake Fasalin Tsaron Jihar

0 106

Sabon gwamnan jihar Zamfara da aka rantsar, Dr Dauda Lawan-Dare a jiya ya bayyana cewa zai hada kai da gwamnatin tarayya da jihohin da ke makwabtaka da jihar domin sake fasalin tsarin tsaro na jihar.

A jawabinsa na karbar rantsuwar kama aiki, gwamnan ya ce matsalar tsaron jihar abin damuwa ce ga kowa da kowa.

Ya ce sabuwar gwamnatinsa za ta mai da hankali sosai kan harkokin tsaro ta hanyar tuntubar gwamnatin tarayya da ma makwabtan jihohin Sokoto, Katsina, Kebbi, Kaduna da Neja.

Gwamnan ya ce hadin gwiwar zai baiwa jihar damar samar da hanyoyin da za a bi domin magance matsalolin da suka addabi yankin na ‘yan fashin daji, da masu garkuwa da mutane da satar shanu da suka kawo koma baya ga ci gaban tattalin arzikin jihar.

Dauda Lawan-Dare ya yi alkawarin tallafa wa jami’an tsaro a jihar da kayan aikin da suka dace domin bunkasa ayyukansu na yakar miyagun laifuka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: