Gwamnan Jihar Taraba Agbu Kefas A Jiya Ya Yi Alkawarin Tunkarar Kalubalen Tsaro A Jihar

0 84

Gwamnan jihar Taraba Agbu Kefas a jiya ya yi alkawarin tunkarar kalubalen tsaro na cikin gida da na waje a jihar.

Agbu Kefas, yayin jawabinsa na farko a filin wasa na Jolly Nyame da ke Jalingo, babban birnin jihar, ya bayyana cewa rashin tsaro ya addabi jihar Taraba sosai a shekarun baya.

Gwamnan ya yi alkawarin hada kan masana harkokin tsaro, da masu ruwa da tsaki, da masarautun gargajiya, da kwararru da matasa domin magance matsalar rashin tsaro.

Ya kuma bayyana cewa gwamnatin sa za ta bai wa matasa aikin yi, da bawa mata jari da kuma tallafawa masu nakasa.

Ya kuma tabbatar wa da jama’a cewa zai zabi wadanda suka cancanta ne kadai domin kafa majalisar ministocinsa.

Agbu Kefas ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da bin diddigin al’amura da kuma daukar nauyin al’ummar jihar yayin da kofofinsa za su kasance a bude domin karbar adawa mai ma’ana.

Leave a Reply

%d bloggers like this: