Amurka Da Saudiyya Sun Yi Maraba Da Tsawaita Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta A Kasar Sudan

0 84

Amurka da Saudiyya sun yi maraba da tsawaita yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakanin bangarorin da ke rikici da juna a kasar Sudan na tsawon kwanaki biyar.

Gwamnatocin Amurka da Saudiyya sun sanar da sabuwar yarjejeniyar, tare da kulla yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka shafe mako guda ana yi.

A cikin wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar, sun amince cewa ba a kiyaye yarjejeniyar tsagaita bude wuta sau da kafa, amma sun ce ta ba da damar kai kayan agaji ga mutane miliyan biyu a Sudan.

Hukumar samar da abinci ta duniya ta ce saukin da aka samu a fadan ya ba ta damar aika kayayyaki ga mazauna babban birnin kasar, Khartoum, a karon farko tun bayan barkewar fadan makonni shida da suka gabata. Sojojin kasar Sudan da abokan hamayyarsu na dakarun RSF sun zargi juna da laifin yawaita take yarjejeniyoyin tsagaita wuta musamman a yankin Darfur.

Leave a Reply

%d bloggers like this: