An Ji Karar Tashin Bama-bamai A Kyiv Babban Birnin Kasar Ukraine

0 69

An ji karar tashin bama-bamai a Kyiv babban birnin kasar Ukraine kuma an kona gine-gine da dama bayan da Rasha ta kai hari a birnin, a dare na uku a jere.

Jami’ai sun ce tarkacen baraguzai ne ya haddasa gobarar, yayin da jami’an tsaron saman Ukraine suka kama jiragen sama marasa matuki guda 20 kuma akalla mutum guda aka ruwaito ya mutu.

A Moscow babban birnin kasar Rasha, wani harin da aka kai da jirage marasa matuki daga baya ya haifar da karamar barna a wasu gine-gine, inji magajin garin birnin.

Rahotanni daga kafafen yada labaran kasar na cewa, an harbo jiragen sama marasa matuki guda 10 a birnin.

Babu dai wata sanarwa daga gwamnatin Ukraine, amma a jiya, shugaban hukumar leken asirin sojin Ukraine ya yi gargadin mayar da martani cikin gaggawa kan jerin hare-haren makami mai linzami da gwamnatin Rasha ta kai kan birnin na Kyiv.

Leave a Reply

%d bloggers like this: