Majalisar Wakilai Ta Yabawa Shugaban Kasa Bola Tinubu Bisa Jajircewarsa Na Cire Tallafin Man Fetur

0 91

Majalisar wakilai ta yabawa shugaban kasa Bola Tinubu bisa jajircewarsa na cire tallafin man fetur da nufin yiwa Najeriya hidima da gaskiya da rikon amana.
Hakan ya biyo bayan amincewa da kudirin gaggawa mai muhimmanci ga jama’a wanda Abdulraheem Olajide na jam’iyyar APC daga jihar Legas ya gabatar a zauren majalisa yau a Abuja.
Da yake gabatar da kudirin, Abdulraheem Olajide ya ce, Shugaba Tinubu dattijo ne mai nuna damuwa wanda manufarsa ita ce nuna goyon baya ga marasa karfi domin jin dadin bil’adama.
Ya ce ya kamata a lura da cewa babu wani tanadi na tallafin man fetur a cikin dokar kasafin kudi ta 2023, inda ya ce majalisar ta 9 da gwamnatin da ta shude sun bawa tallafin goyon baya a doka.
Majalisar ta taya shugaban kasar murna bisa shirye-shiryen da ya ke yi na ayyukan da ke gabansa na hidimtawa jama’a.
Majalisar ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su kasance masu hakuri da juriya da addu’a domin shugaban kasar ya cika alkawuran da ya dauka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: