Alkalin Wata Kotu Ya Bayyana Cewa ASUU Ba Ta Da Hakkin A Biya Ta Albashi A Tsawon Lokacin Da Ta Ke Yajin Aikin Ta

0 78

Kotun masana’antu ta kasa a yau ta bayyana cewa matsayin gwamnatin tarayya na rashin biyan albashi ga kungiyar malaman jami’o’i, ASUU, a lokacin da suke yajin aiki, ya halatta.
Da yake yanke hukuncin, mai shari’a Benedict Kanyip ya bayyana cewa ASUU ba ta da hakkin a biya ta albashi a tsawon lokacin da ta ke yajin aikin.
Benedict Kanyip ya bayyana cewa gwamnatin tarayya da ministan ilimi wadanda su ne wadanda ake kara sun yi kuskure da suka nemi kotu ta kakabawa kungiyar ASUU takunkumi saboda tafiya yajin aiki na lumana.
Alkalin ya bayyana hakan a matsayin babban cin zarafi ga ‘yancinsu na gudanar da kungiyar kamar yadda dokar kungiyar kwadago ta kasa da kasa ta tanada.
Kotun ta kuma ce masu da’awar ba za su iya tilasta wa ASUU karbar albashin mambobinta ta hanyar IPPIS ba, muddin sun tabbatar da kasafin kudinsu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: