Majalisar wakilai ta ba da shawarar yin gyara ga dokar laifuka ta 2004 don rage hukuncin yunƙurin kashe kai a Najeriya

0 193

Majalisar wakilai ta ba da shawarar yin gyara ga dokar laifuka ta 2004 don rage hukuncin yunƙurin kashe kai a fadin kasar nan.

Wannan ya biyo bayan wani kudurin dokar da ya wuce karatu na biyu ne a zaman majalisar da aka gudanar a jiya.

Da ya nemi a gyara sashi na 327 da ya ba da shawarwari na tilas da yi wa al’umma hidima na tsawon wa’adin da bai wuce watanni 6 ba.

Sabanin daurin shekara 1 a gidan yari da ke kunshe a cikin dokar da ake da ita a halin yanzu

Ko da yake ba a yi muhawara kan kudirin dokar ba, kwafin muhawarar ya nuna cewa, wanda ya dauki nauyinsa, Rep. Ejiro Waive, na da ra’ayin cewa masu kashe kansu nada matukar bukatar magunguna da shawarwari masu inganci.

Ya kuma kara da cewa mafi akasarin masu yunkurin kashe kansu suna a cikin halin neman taimako ne.

Leave a Reply

%d bloggers like this: