Makki Yellemen yana zawarcin ofoshin kakakin Majalisa ta 10.

0 115

Dan wajalisar wakilai, Abubakar Makki Yellemen ya shiga neman kujarar ofoshin kakakin Majalisai ta 10.

Makki Yelleman mai wakiltar kananan hukumomin Malam-Maduri da Kaugama a zauran majalisar wakilai wanda yanzu haka shine mataimakin shugaban kwamitin tsaro na majalisar.

Ya nuni da cewa, tsarin shiyya-shiyya na shugabancin majalisar wakilai na jam’iyyar APC mai mulki, wanda ya rike rinjaye a majalisar dattawa da na majalisar wakilai, shi ne zai tantance mukamai da ‘yan majalisar za su yi takara.

Ya kuma bukaci jam’iyyar APC data mika shugabancin Majalisar ga arewacin kasar nan, yana mai cewa hakan zai kara inganta adalci da daidaiton a siyasa kasar nan.

Da yake zantawa da yan jarida yau a Abuja dan majalisar yace zai nemi kujerar kakakin Majalisar ta 10. Makki yace yana fatan kujerar zata kasance a arewa ta tsakiya ko arewa maso yammacin kasar nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: