Ku Cigaba da Taimakawa Sabbin Shuganni Masu Jiran Gado da Addu’a – Masari

0 107

Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya jaddada cewa akwai bukatar yan Najeriya su ci gaba da taimakawa sabbin shugabannin dasu karbi ragamar mulki nan gaba da addu’a domin shugabancin da zai ciyar da kasar nan gaba.

A cewar Masari,shugabanni na bukatar addu’ar yan kasa domin yiwa kasa aiki.

Masari na wannan jawabi a jiya a dakin taro na Muhammadu Buhari dake kastina, yayin da ya shirya taron addu’o’I na musamman ga zababben shugaban kasa Bola Ahmed da mataimakin sa Kashin Shettima da kuma zababben gwamnan jihar Katsina Dr Dikko Umar Radda, da mataimakin sa Faruk Lawan Jobe da yan sauran yan majalissu.

Taron addu’ar ya samu halattar manyan malamai da shugabannin addini da ke fadin jihar, inda suka taru domin nuna Godiya ga Allah da ya zabin shugabanni na nagari. Malaman addini da suka halarci taron addu’ar sun yi kira ga sabuwar gwamnati mai zuwa a jihar data kwai-kwayi shugabanci nagari irin Gwamnan jihar Aminu Bello Masari domin a samu sakamako mai kyau, tare da yin addu’a Allag ya taimaki sabuwar gwamnatin wajen yin abinda ya dace.

Leave a Reply

%d bloggers like this: