Malamai dubu 2,000 sun hadu a Kano domin yi wa Tinubu addu’ar samun nasara a 2027

0 135

Dan Majalisar Tarayya daga Jihar Kano, Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa, ya hada malamai da limamai sama da 2,000 domin gudanar da addu’o’i na musamman ga Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da kuma gwamnatin sa gabanin zaɓen shekarar 2027.

An gudanar da taron addu’ar ne domin neman zaman lafiya, ci gaban ƙasa da kuma nasarar gwamnatin tarayya wajen aiwatar da manufofinta.

Rahotanni sun ce malaman sun yi addu’o’i tare da roƙon Allah Ya kawo kwanciyar hankali, arziki da haɗin kai a Najeriya baki ɗaya.

Haka kuma, an bayyana cewa an yi addu’o’in ne domin samun nasara ga Shugaba Tinubu da kuma Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, a zaɓen shekarar 2027.

Leave a Reply