Manyan jiga-jigan yan siyasa a kasarnan sun bayyana farincikinsu dangane da tabbatar da tsohuwar ministar kudi, Dr Ngozi Okonjo-Iweala, a matsayin mace ta farko kuma yar Afirka ta farko da aka ambata a matsayin Darakta Janar ta kungiyar cinikayya ta duniya, WTO.

Babban mai taimakawa shugaban kasa akan kafafen yada labarai da hulda da jama’a, Garba Shehu, ya rawaito shugaban kasa Muhammad Buhari yana taya ta murna.

Ya rawaito shugaban kasar na cewa cigaban ya haifar da farinciki da karin martaba ga kasarnan.

Kazalika, Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmed Lawan, a wata sanarwa daga ofishinsa na yada labarai, ya taya Najeriya murna akan abin alkhairin da ya samu mace ‘yar asalin Najeriya a matakin duniya. Kakakin Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila, da kungiyar marasa rinjaye a majalisar, suma sun taya murna ga sabuwar Darakta Janar ta kungiyar cinikayya ta duniya.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: