An yi bikin rantsar da Fafaroma Leo XIV a fadar Vatican a ranar Lahadi, 18 ga watan Mayu, 2025. Manyan shugabanni daga kasashen duniya daban daban sun halarci bikin shan rantuwar da sabon Fafaroman ya yi.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya halarci bikin rantsar da sabon shugaban cocin Katolika na duniya, Fafaroma Leo XIV, a dandalin St. Peter da ke birnin Vatican a Rome a kasar Italiya.
Bikin ya kasance na musamman domin yana nuna fara jagorancin sabon Fafaroma bayan rasuwar Fafaroma Francis. Tinubu ya samu gayyata ne daga Fafaroma Leo XIV, wanda ya bayyana Najeriya a matsayin kasa da ta kasance kusa da zuciyarsa tun lokacin da ya taba aiki a Ofishin Jakadancin Vatican a Lagos.
Vanguard ta wallafa cewa shugaba Tinubu ya bayyana cewa halartar bikin yana daga cikin kokarinsa na karfafa hadin kai da fahimtar juna a Najeriya, yana mai cewa, Yana daga cikin hanyar hadin kai duk da bambance bambancenmu.