Masarautar Hadejia ta sauke Hakimin ta, Dan Lawan din Hadejia

0 838

Masarautar Hadejia a jihar Jigawa ta sauke wani mai rike da sarautar gargajiya Alhaji Abubakar Hussain Abubakar a daga matsayin Dan Lawan na Hadejia.

Majiyar mu ta ruwaito jami’in hulda da jama’a na majalisar Muhd ​​Garba Talaki ya bayyana cewa, wata takarda mai dauke da sa hannun sakataren majalisar Alhaji Muhammad Baffale Abbas ta tabbatar da korar ta sa biyo bayan huldar sa da miyagun kwayoyi. Ya ce majalisar ta tabbatar da lamarin ta hanyar wata wasika da ta samu daga hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa reshen jihar jigawa da ke sanar da majalisar kan lamarin.

Ya ce hakimin ya ki girmama takardar gayyata da Majalisar Masarautar ta aike domin ya bayyana a gaban ta ya kare kansa.

Don haka Sakataren masarautar, Alhaji Muhammad Baffale ya shawarci jama’a musamman masu mu’amala da shi a kan haka da su lura. Ya ce an dauki wannan tsauraran matakin ne domin ya zama ishara ga sauran Shugabannin Gargajiya, ya kuma bukaci shugabannin gargajiya na yankin da su kasance masu da’a ga Masarautar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: