Tsohon Kwamishina a Jihar Kano ya soki bukatar binciken Ganduje

0 251

Tsohon Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Malam Muhammad Garba, ya maida martani kan zargin da ake yi cewa tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje ya karbo rancen Naira biliyan 10 domin kafa kyamarori domin samar da tsaro a jihar.

Mallam Garba ya mayar da martani ne ga wata kungiyar hadin kan al’umma, wadda rahotanni suka bayyana cewa ta yi wannan ikirarin.

Garba ya soki bukatar binciken Ganduje, yana mai cewa ikirarin kungiyar wani yunkuri ne na bata sunan tsohon gwamnan.

Ya ce suna kalubalantarsu da su ba da wata shaida kan bashin Naira bilyan goma domin kuwa a cewar lokacin da gwamnatin tayi wannan aikin Majalisar Zartarwa ta Jiha da Majalisar dokokin jihar sun ba da izini a hukumance, tare da la’akari da mahimmancin aikin da nufin inganta tsaro a jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: