An kafa kwamitin kwato filaye da gonakin da aka yanka ba bisa ka’ida ba a Jigawa

0 598

Gwaman Umar Namadi Danmodi ya kafa kwamiti kwato filaye da gonakan da aka yanka ba tare da izinin gwamnati ba.
Kafin hakan dai anyi zargin cewa an yanka wasu filaye da gonakai tare da rabawa wasu kamfanoni da daidaikun mutane ba bisa ka’ida ba.
Yayin kaddamar da kwamitin karkashin jagoranci sakataren gwamnatin jiha Mallam Bala Ibrahim (Mamser), gwamnan yace ya dauki wannan matakin ne domin tabbatar da bin doka da oda wajen aiwatar da kowanne mataki.
A cewarsa ya dauki wannan matakin ne domin magance faruwar rikicin manoma da makiyaya musamman a lokacin rani.
Idan zamu iya tunawa dai Gwamna Umar Namadi Yasha alwashin tabbatar da gaskiya da adalci a gwamnatin sa.
A daya bangaren kuma Gwamna Umar Namadi ya kafa wani kwamitin da zaiyi bincike akan shirin rabon kudi na FADAMA III, gwamnan ya nada shugaban ma’aikatan gidan gwamnati Sanata Mustapha Makama a matsayjn shugaban kwamitin tare da kira a gare shi da sauran mambobin da suyi aiki babu sonkai wajen gudanar da binciken.

Leave a Reply

%d bloggers like this: