Ana cigaba da musayar ra’ayoyi kan batun karin kudin man fetur

0 240

Ana ci gaba da musayar ra’ayoyi da Allah wadai kan matakin karin farashin man fetur daga naira 540 zuwa naira 617 kowace lita na baya-bayan nan.

Shugaban kungiyar kwadago na kasa Joe Ajaero a jiya ya ce ana yaudarar ‘yan Najeriya kan batun farashin man fetur.

Ajaero, wanda ya bayyana haka a cikin wani shirin talabijin na kai tsaye, ya ce ana azabtar da talakawa babu gaira babu dalili.

Jam’iyyar PDP ta bayyana karin farashin man fetur na baya-bayan nan a matsayin tsokana.

Sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP na kasa, Debo Ologunagba a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce tsarin farashin da ake yi a halin yanzu wani tsari ne da kowa a fadin kasa ke Allah wadai dashi, bisa nuna rashin tausayi ga ‘yan kasa, yana mai zargin cewa gwamnati na son ganawa mutanen da tuni ke shan wahala ukuba.

Haka kuma, babban taron jam’iyyun siyasar kasa CNPP ya ce karin farashin man fetur ba kakkautawa na nuni da cewa gwamnatin APC ba ta taba yin gaskiya da ‘yan Najeriya ba kan batun tallafin.

Sai dai Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bukaci ‘yan kasa da su ci gaba da fatan samun ci gaba yayin da suke jajircewa wajen tunkarar kalubalen da suke fuskanta da kuma radadin wucin gadi da suke fuskanta. Tinubu, wanda ya taya al’ummar Musulmi murnar shiga sabuwar shekarar Musulunci, ya ce shi da tawagarsa ba su bar wani abu ba a wani yunkuri na cika alkawuran da aka dauka duk da matsalolin da ake fuskanta a yanzu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: