Masu yin NYSC da hadin gwiwar Gidauniyar Yushe’u Abdu, sun yiwa Mutane 200 gwajin Lafiya a Dutse

0 62

Hukumar Matasa Masu yiwa Kasa Hidima, tare da hadin gwiwar Gidauniyar Yushe’u Abdu, sun yiwa Mutane 200 gwajin Lafiya tare da bada Magani kyauta a garin Kachi na karamar hukumar Dutse ta nan jihar Jigawa.

Shugabar Hukumar ta JIhar Jigawa Hajiya Aishatu Adamu, ita ce ta bayyana hakan a lokacin kaddamar da aiki a birnin Dutse.

A cewarsa Matasa tare da hadin gwiwar Gidauniyar sun samarda magunguna da sauran kayan aiki ga mutanen garin.

Haka kuma ta ce shugaban Gidauniyar dan asalin garin na Kachi ne, inda ya tallafawa Matasan na NYSC domin gudanar da aikin.

Hajiya Aisha Adamu, ta ce aikin ya bankado illolin rashin tsaftar muhalli da kuma kulawa da Lafiya.

Kazalika, ta ce shirin zai bada kariya daga cin gurbatattun abinci da kuma ruwan sha.

A jawabinsa, Daraktan Kudi da Mulki, na Hukumar Fansho da Albashi ta jihar Jigawa, Alhaji Yusha’u Abdu, wanda kuma shine shugaban Gidauniyar, ya godewa Matasan bisa yadda suka gudanar da aikin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: