Mataimakin Shugaban Kasa Osinbajo ya shaida wa Shugaba Buhari aniyarsa ta tsayawa takara a zaben 2023

0 81

Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya shaida wa Shugaba Muhammadu Buhari aniyarsa ta tsayawa takara a zaben 2023 mai zuwa, kamar yadda wasu majiyoyi suka tabbatar wa Aminiya.

A cewar majiyoyin, Osinbajo na son karbar ragamar Shugabancin kasar ne bayan karewar wa’adin Buhari a 2023 don dorawa kan nasarorin da suka samu bayan karbar mulkinsu daga PDP a 2015.

Kodayake har yanzu bai bayyana aniyarsa tasa a hukumance ba, hakan na nufin ke nan zai fafata da jagoran jam’iyyar APC na kasa, kuma tsohon Gwamnan Jihar Legas, wanda shi ma a ’yan watannin baya ya ziyarci Buharin sannan ya shaida masa aniyarsa ta tsayawa takarar.

Wata Majiyar Shugaba Buhari ya yi masa fatan alheri kamar yadda ya yi wa Tinubu lokacin da ya ziyarce shi a Fadar Shugaban Kasa don samar masa da aniyarsa.

Kazalika, wata majiyar ta ce lokacin da Osinbajon ya tunkari Buhari da maganar, bai nuna mamaki ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: