Ministan Harkokin Lantarkin na Kasa ya kira taron gaggawa na masu ruwa-da-tsaki domin samo mafita dangane da matsalar wutar lantarki

0 46

Ministan Harkokin Lantarkin na Kasa, Inijiniya Abubakar D. Aliyu ya kira taron gaggawa na masu ruwa-da-tsaki domin samo mafita dangane da matsalar wutar lantarki da ta tsawwala a ‘yan kwanakin nan.

Taron ya kunshi kamfanonin samar da wutar lantarki da kuma hukumomi na gwamnati da masu zaman kansu da suke da ruwa da tsaki a harkar samar da wutar lantarki da iskar gas.

A wurin taron, wanda aka gudanar a Abuja, Injiya Abubakar D. Aliyu ya ce gwamnati ba za ta amince ba da yadda lamarin wutar lantarki ya samu koma-baya, yana mai cewa dole a samo mafita ga dukkan matsalolin da suke kawo koma-baya ga yawan wutar lantarki da ‘yan Najeriya suke samu a kullum.

Ministan ya kuma gargadi hukumomi da kamfanoni na harkar wutar lantarki su guji nunawa juna yatsa, tare da mayar da hankali wajen tallafawa juna domin tabbatar da cewa ‘yan Najeriya suna samun isasshiyar wutar lantarki.

Taron ya mayar da hankali ne ga duba dukkan matsalolin da suke kawo koma-baya ga harkar wutar lantarki a Nijeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: