Hukumar Shirya Jarabawar Kammala Sikandiren Kasuwanci da Fasaha ta Kasa (NABTEB) ta bayyana cewa kimanin Dalibai dubu 29,915 ne suka ci Jarabawar a bana, ta hanyar samun Kiredit 5 ciki harda Turanci da Lissafi, daga cikin dubu Dalibai dubu 38,639 da suka rubuta Jarabawar a watan Mayu/Yuni na 2021.

Shugabar Hukumar Farfesa Ifeoma Isiugo-Abanihe, shine ya bayyana hakan a birnin Benin bayan sakin sakamakon Jarabawar ta shekarar 2021.

A cewarta, Dalibai dubu 29,915 sun samu Kiredit 5 ciki harda Turanci da Lissafi, sai kuma Dubu 29,923 da suka samu Kiredit 5 babu turanci da Lissafi.

Haka kuma ta ce Dalibai 197 ne aka samu da laifin satar amsa a lokacin rubuta Jarabawar.

Shugabar Hukumar ta ce kimanin Dalibai dubu 38,793 ne suka yi Rijista domin rubuta Jarabawar, sai dai dubu 38,639 ne kadai suka rubuta Jarabawar a Cibiyoyi dubu 1,696 da suke kasar nan.

Farfesar ta bukaci Iyaye su garzaya cibiyoyin duba Jarabawar ta NABTEB domin sanin abinda yayan su suka rubuta.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: