Hukumar Samarda Ruwan Sha ta Jihar Bauchi ta rage Ruwan da take samarwa daga Liti Miliyan 60 zuwa Miliyan 30 a kullum

0 56

Biyo bayan Karancin Wutar Lantarki a Kasa baki daya, Hukumar Samarda Ruwan Sha ta Jihar Bauchi ta rage Ruwan da take samarwa daga Liti Miliyan 60 zuwa Miliyan 30 a kullum.

Shugaban Hukumar Samar da Ruwan Sha ta Jihar Bauchi Alhaji Aminu Gital, shine ya bayyana hakan tare da bayyana damuwa kan matsalar.

A cewarsa, duk da cewa lamarin wutar ya fara daidaita, amma kuma Karfin wutar bazai iya turo Ruwan da birnin Bauchi ya ke bukata ba.

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN) ya rawaito cewa saboda karancin Ruwan sha, mutane da dama a cikin garin Bauchi na cikin damuwa bisa matsalar.

Alhaji Aminu Gital ya ce Hukumar ta na hada hannu da sauran hukumomin gwamnati domin daidaita lamura a Jihar.

Haka kuma, ya bukaci masu amfani da Ruwan su kasance masu fahimta, a lokacin da hukumar take kokarin daidata lamuran.

Leave a Reply

%d bloggers like this: