Sarkin Kano ya bukaci yan kasuwar jihar Kano da kada su kara farashin kayan masarufi saboda zuwa watan Ramadana

0 79

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, ya bukaci yan Kasuwar Jihar da kada su kara farashin kayan Masarufi saboda zuwa watan Ramadana.

Sarkin ya yi wannan kiran ne a lokacin da ake gudanar Addu’oi na musamman kan cikarsa shekaru 2 akan Karagar Mulkin Masarautar.

Alhaji Aminu Ado Bayero, ya godewa Allah Subhanahu wata Ala, bisa damar da ya bashi na Jagorantar Al’umma, inda ya bukaci yan kasuwar su ji tsoron Allah karsu kara farashin.

Haka kuma ya godewa Gwamnatin Jihar Kano da Mambobin Majalisar Masarautar da kuma Al’ummar Kano bisa hadin kan da yake samu.

An gudanar da Addu’oi a babban Masallacin Kano, wanda babban Limamin Kano Farfesa Muhammad Sani Zahraddeen da Wazirin Kano Alhaji Sa’ad Shehu Gidado, suka jagoranta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: