A kokarin jan hankulan ‘yan Najeriya kan amincewa da allurar rigakafin cutar corona, Kungiyar ECOWAS ta bukaci gwamnati da ta dauki mataki na biyan diyya ga duk wanda ya fuskanci duk wata matsala a sakamakon yin allurar.

A yayin zaman kotun karkashin jagorancin Mai Shari’a Sulaiman Baba Na Malam, a ranar Litinin, lauyan Jaafar Jaafar da na jaridar Penlight sun soki yadda masu wakiltar bangaren Ganduje suka kawo sabbin lauyoyi sabanin wadanda aka fara shari’ar da su tun fil azal.

Aminiya ta samu cewa, Mai Shari’a Na Malam ya yi watsi da sukar lauyoyin masu karar suka yi, inda kuma ya sake dage sauraron karar zuwa ranar 20 ga watan Afrilun 2021.

Kamar yadda Gidan Rediyon Freedom mai tushe a Kanon Dabo ya ruwaito, ya ce lauyoyin Gwamna Ganduje sun ce ba sababbin lauyoyi suka kawo ba, illa iyaka kari ne a kan lauyoyin da suke kare su.

Shi kuwa lauyan Jaafar Jaafar, U. U Ete cewa ya yi, sun yi sukar ne ganin yadda aka zo da sabbin fuskoki a madadin Barista Nura Ayagi da aka fara shari’ar da shi tun usuli.

https://www.dw.com/ha/matakin-biyan-diyyar-corona-ka-iya-karfafa-guiwar-jamaa/a-56806739

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: