Hukumar Tsaro ta NSCDC reshen jihar Kwara ta kama mutane hudu a Karamar Hukumar Irepodun bisa zargin yi wa wata mata fyade sannan daga bisani suka kasheta.

Rahotanni sun ce daga bisani an tsinci gasar matar, mai suna A’isha Sani a cikin daji bayan da jami’an tsaro suka bazama nemanta.

Wadanda ake zargin dai a cewar Kakakin hukumar ta NSCDC a jihar ta Kwara, Babawale Zaid Afolabi matasa ne masu shekaru 19 da 16 da 15 da kuma 16.

Ya ce sakataren Kungiyar Fulani na Esie/Ijan, Alhaji Musa Waziri ne ya kai rahoton zuwa ofishin hukumar.

Babawale ya kara da cewa an tsinci gawar A’isha tsirara ne da misalin karfe 8:30 na safiyar ranar hudu ga watan Fabrairun 2021 da raunuka a sassan jikinta da dama.

“Mun kama uku daga cikin wadanda muke zargi kuma a bayanansu sun nuna cewa sun kama wata mata ’yar Fulani ce bisa zargin satar Kashu amma daga baya ta tsere.

“Buncikenmu ya gano cewa babban wanda ake zargi ya aika sauran masu aika-aikar su uku su kamo masa daya matar saboda ya yi amfani da ita.

“A kokarinsu na yi mata fyaden, ta sami nasarar ji masa rauni a kafadarsa ta dama da kuma wuyansa,” inji shi.

Ya ce tuni aka tisa keyar wadanda ake zargin zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka domin fadada bincike.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: